B-kebbi: Shiyar Nahuta a bayan kara na bukatar caben wutan lantarki

Unguwar bayan kara da ke cikin garin Birnin kebbi daya ce daga cikin unguwannin da ke taga masu shi sakamakon bunkasar gari ta wannan bangari sakamakon yawan fadin kasa da inganci wanda hakan ya sa unguwar ya sami karbuwa ga masu son gina sabin gida.

Wannan unguwa akwai saukin samun ruwa matukar za ka yi rijiyar zamani na borhole da kan ka, sakamakon taushin kasa da ke sjhinfide a wannan unguwa da yashi ke da rinjaye.

Amma akwai wata matsala da ta dabaibaye unguwar, musamman gangaren karshen sabon titin unguwar na baayan kara, matsalar ita ce ta rashin ingancin cabe na wuutan lantarki.

Caben wutan lantarki a unguwar musamman a shiyar Kwanar yan suya cabe ne da basa da inganci.Haka zalika lamarin ya mamaye shiyar har zuwa shiyar Nahuta da ke bayan kara.

Galibin caben ko dai katako ne ko dogayen itatuwan wuta aka rataya masu wayan lantarki wanda lokaci zuwa lokaci sukan sami matsala da ke haifar da daukewar wutan lantarki a shiyar.

Duk da yake Gwamnati ta saka wasu karin kananan transfomomi a unguwar musamman a kan cabe da suka dauko babban wayan wutan lantarki a gefen titin Bayan kara, amma akwai bukatar Gwamnati ta waiwayi unguwar na Bayan kara domin a taimaka wa mazauna shiyar Kwanar yan suya da Nahuta cabe na wutan lantarki domin su ma su wadata da lantarki.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN