• Labaran yau


  Wani babban dan siyasar Jamus ya karbi Addinin Musulunci

  Mataimakin shugaban jam'iyyar AfD ta 'yan mazan jiya na jihar Brandenburg ta kasar Jamus Arthur Wagner ya rungumi Addinin Musulunci.

  Mataimakin shugaban jam'iyyar AfD ta 'yan mazan jiya na jihar Brandenburg ta kasar Jamus Arthur Wagner ya rungumi Addinin Musulunci.

  Jaridar Tagesspiegel ta bayar da labarin cewa, ba da jima wa ba Wagner ya Musulunta.

  A labaran da aka fitar an sanar da cewa, Wagner ya ki ya yi dogon jawabi game da karbar Addinin Musulunci da ya yi inda ya ce, batu ne da ya shafe shi.

  Shugaban Majalisar Shura ta jam'iyyar AfD Andreas Kalbitz ya ce, tabbas da gaske ne Wagner ya Musulunta.

  Kalbitz ya kuma ce, a ranar 11 ga watan Janairu ne Wagner ya sanar da ficewar sa daga majalisar gudanarwar jam'iyyar AfD a jihar Brandenburg.

  Kakakin jam'iyyar na jihar daniel Friese ya ce, zabin mutane ne su shiga Addinin da suke so.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wani babban dan siyasar Jamus ya karbi Addinin Musulunci Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama