• Labaran yau


  B-kebbi: Saurayi ya waska wa mai kayan miya mari ya ruga da gudu

  Yan kwanaki da suka gabata a unguwar Nassarawa2 da ke garin Birnin kebbi wani lamari mai ban haushi da ya jibanci matakin farko na tabarbarewar tsaro daga zuciyar wani saurayi, domin wannan saurayi ya je ne a kan babur tare da wani saurayi dogo, sai daya saurayin ya waska ma wani mai sana'ar sayar da kayan miya mari sai ya ruga da gudu.

  Bayanai sun nuna cewa shi wannan saurayi ya mari wani karamin yaro ne wai domin ya ratsa a tsakaninsa da abokansa yayin da suke zance,ganin haka ne ya sa kawun yaron wanda shi ne mai sayar da kayan miya ya je ya tambayi saurayin musabbabin da ya sa ya mari yaro shi kuma ya kasa bayar da hujja. Sakamakon haka sai kawun yaron ya rama wa yaron marinsa ta hanyar marin saurayin.

  Daga bisani sauraayin ya dawo dadai lokacin magariba tare da wani saurayi dogo,sai saurayi dogo ya yi wa mai kayan miya sallama ta hanyar mika masa hannu domin su yi musabaha.Mika hannunsa ke da wuya sai saurayi ya waska masa mari daga bayansa,yayin da mai kayan miya ya yi kokarin ya kubuce hannunsa daga hannun saurayi dogo sai dogo ya rike hannun mai kayan miya daram ya hana shi domin ya bi wannan saurayin.

  Wannan lamari ya haifar da fargaba akan tsaro, domin wannan lamari ya yi kama da shiri inji wani mai fashin baki kan harkar tsaro. Ya ce ya kamata a kama saurayi da ya aikata wannan lamari domin a gane ko dan kungiyar bata gari ne ko dan kungiyar masu aikata laifi. Amma jama'a sun ba mai kayan miya hakuri shi kuma ya lamunce.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: B-kebbi: Saurayi ya waska wa mai kayan miya mari ya ruga da gudu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama