• Labaran yau


  Kotu ta kai basarake kurkuku bisa zargin damfaran N550.000

  An gurfanar da wani basaraken gargajiya mai suna  Alhaji Muhammadu Uba Wuntin Dada a gaban wata babban Kotu a birnin Bauchi bisa zargin damfara akan kudin filaye bayan an tuhume shi da karbar N550.000 daga hannun wani mutum a 2013 kasancewar kudin wani fili daga bisani kuma ya sake sayar da filin ga wani mutum daban.

  Bayanai sun nuna cewa basaraken ya yaudari mutum na biyu cewa filin nashi ne bayan ya riga ya saida filin ga mutum na farko.

  Alkali Shitu na babban Kotun ya bayar da belin basaraken tare da dage shari'ar zuwa ranar 12 ga watan Maris 2018. Koyu ta tasa keyar basaraken zuwa Kurkuku kafin ya cika ka'idodin beli.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kotu ta kai basarake kurkuku bisa zargin damfaran N550.000 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama