Auren 'yan Luwadi a Makka, yansanda sun kama wadanda suka daura auren

Hukumomin 'yansanda a birnin Makka na kasar Saudiya sun kama wasu mutane da suka bayyana a wani faifan bidiyo wanda aka ce biki ne na daurin auren wasu 'yan luwadi. Hakan ya biyo baya wata sanarwa da 'yansanda suka fitara a shafinsu na twitter a kasar ta Saudiya.

A cikin faifan bidiyon an ga wasu mutane 'yan daudu tare da daya saurayin saye da tufa wanda ya yi kama da na Amarya yayin da suke takawa irin na Amarya da Ango.

Sanarwar 'yansandan ta ce wani mutum ne ya tsegunta masu cewa ana gudanar da wani biki ne sai wasu mutane suka yi mafani da wannan damar suka gudanar da daurin auren 'yan luwadi  kuma bisa wannan labarin 'yansanda suka kai samame ga wadanda suka halarci daurin auren.

Aikata luwadi a kasar Saudiya dai yana dauke da matsanancin  hukunci wanda ya jibanci bulala ko kisa.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN