Ababe 8 da za ka kaurace a rayuwar ka domin samun kwanciyar hankali

Jayewa daga wani guri ko wani abu ba tsoro bane ko nusaranci, amma zai iya kasancewa wani tsari da salo na kawar da wata damuwa ko yanayi da zai iya rikidewa ya zama kazamtaccen lamari da ba a so ya faru.

Ga wadannan ababe da ya kamata ka kula a rayuwar ka :

1. Ka kaurace wa gardama maras ma'ana da kuma baya da fa'ida

2. Ka kaurace wa mutane da suke kokarin ganin bayan ka  da gangan

3. Ka kaurace ma duk wani tunani da ba zai kai ka ga nassara ba

4. Ka kaurace ma duk wani lamari da zai iya kai ka ga damuwa

5. Ka kaurace wa duk wanda baya son ka musamman wanda dama ce kawai ya samu a rayuwa

6 . Matukar ka kaurace ma duk lamari da ke iya zama guba ga rayuwar ka, lallai za ka sami sa'ida a rayuwar ka.

7. Ka tsara ma kanka nishadin zuciya, kaurace ma kitsa sharri da mugunta a zuciyarka, yi tunanin alhairi ka kyale mai aikata sharri da sharrinsa.

8. Ka yi ibada ga Allah ba wai don wani ya gani ba domin da yawa cikin masu da'awa da sunan addini munafunci ya yi katutu a zukatansu, sau da yawa sukan haye nasu laifin domin su hango na wani. Idan kuma basu hango ba sai su kirkiro laifin domin su ja hankalin jama'a.

Isyaku Garba 

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN