• Labaran yau

  An sake kira ga makiyaya su zauna lafiya da manoma a Aljannare

  Mataimakin gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai ya ziyarci al'umman Fulani ranar Alhamis a garin Aljannare inda ya bukaci su kasance masu jin tsoron Allah da kuma kasancewa masu son zaman lafiya domin tabbatar da tsaro mai inganci tsakanin manoma da makiyaya a wannan yankin. Ya yi wannan jawabi ne ga shugabannin,dattijai da suran manyan al'umman Fulani a lokacin ziyarar.

  Alh. Samaila Yombe ya shaida wa al'umman Fulani cewa ya wakilci Mai girma Gwamnan jihar Kebbi ne Sanata Abubakar Atiku Bagudu domin isar da sakon gwamna a kan muhimmanci da bukatar zaman lafiya.

  Ya kara da cewa yanzu haka Gwamna Abubakar Atiku Bagudu yana halartar wani taro da shugaban kasa domin ganin an shawo kan lamarin manoma da makiyaya.

  Isyaku Garba

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: An sake kira ga makiyaya su zauna lafiya da manoma a Aljannare Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama