• Labaran yau

  An sallami Yusuf 'dan shugaba Buhari daga asibiti

  Wata sanarwa da ta fito daga hukumar Asibitin Cedarcrest inda aka kai 'dan shugaban kasa Muhammadu Buhari watauYusuf Buhari ta ce 'dan shugaba Buhari watau Yusuf yana murmurewa daga tiyata da aka yi masa sakamakon raunuka da ya samu akan babur kwanakin baya.

  Yusuf ya sami hatsari da babur a ranar 26 ga watan Disanba 2017 a birnin Abuja yayin da yake tsere da babur tare da abokinsa.

  Sanarwar wacce ta fito daga hannun daraktan asibitin Dr Felix Ogedegbe yace nassara da aka samu wajen jinyar Yusuf ya ta'allaka ne bisa ingantattun kayan aiki tare da kwarewa na ma'aikatan asibitin , ya ce haka ya nuna irin nassara da kwarewa da ake da shi a wasu asibitoci a Najeriya.

  Ya kuma kara da cewa ba gaskiya bane jita-jita da aka yi ta yayatawa a shafukan sada zumunta wanda ke nuna cewa hatsarin ya rutsa da abokin Yusuf, ya musanta haka, haka zalika ya musanta cewa hatta uwargidan shugaba Buhari Aisha Buhari ta yi jinya sakamakon matsanancin damuwa dangane da lamarin a asibiti. Ya ce duk wannan jita-jita ne kuma babu kanshin gaskiya.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: An sallami Yusuf 'dan shugaba Buhari daga asibiti Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama