Rundunar 'yansandan jihar Kebbi ta kama yan fashi 41, bindigogi 12, babura 16

Isyaku Garba

Hukumar 'yansandan jihar Kebbi ta yi nassarar damke 'yan fashi da makami guda 41 tare da kama wasu bindigogi kirar hannu guda 12 da albarussai guda hudu har da cartridge guda tara daga Janairu zuwa Disamba 2017.

Kwamishinan 'yansanda na jihar Kebbi Ibrahim Kabiru ya shaida wa manema labarai haka a Birnin kebbi ranar Laraba, ya kuma kara da cewa rundunar ta gurfanar da wadanda ake zargi a gaban Kotu.

Ya ce rundunarsa ta kama baburan sata guda 16 yayin da aka gurfanar da wadanda ake zargi a gaban Kotu inda aka tasa keyarsu zuwa gidan yari yayin da ake ci gaba da shari'a.
Kwamishina Ibrahim ya ce shanaye 131 na sata rundunar ta kama kuma bayan bincike ta gabatar da su ga ainihin masu shanayen. Ya ce rundunarsa za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyar jama'ar jihar Kebbi musamman lokacin bukukuwan Kirsimeti da na karshen shekara.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN