• Labaran yau

  Kotu ta ki bayar da belin Maryam, an sake tasa keyarta zuwa gidan Yari

  Alkalin wani babban Kotun tarayya da ke Abuja Justice Yusuf Haliru ya ki aminta ya bayar da belin Maryam Sanda wacce ake zargi tare da tuhumar kashe maigidanta Bilyamin Bello, sakamakon rashin gamsuwa da hujjoji da Lauyanta ya gabatar a gaban Kotu na neman belinta bayan an gabatar da Maryam yau a gaban Kotun.

  Alkalin ya ce Lauyan Maryam bai gamsar da Kotun ba akan cewa bata da lafiya tare da gabatar da takardar shaidar cewa lallai Maryam bata da lafiya.Alkalin ya ci gaba da cewa Lauyan bai gabatar wa Kotun cewa ko cutar da take fama da shi ba za'a iya jinyan sa ba a gidan yari.

  Haka zalika , Alkalin ya ce zancen cewa Maryam tana shayar da Jaririya wannan ba hujja bane domin a bayar da belinta.

  Amma Kotun ta bayar da belin mahaifiyar Maryam watau Maimuna Sanda, da wani 'dan uwanta bisa sharudda da Kotun ta gitta .

  An dage shari'ar zuwa ranar 5,6,da 7 ga watan Fabrairu 2018 yayin da aka tasa keyar Maryam zuwa gidan yarin garin Suleja.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kotu ta ki bayar da belin Maryam, an sake tasa keyarta zuwa gidan Yari Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });