• Labaran yau

  Labarai a yau

  Jam'iyyar APC mai mulki a Nigeria ta zargi Jam'iyyar adawa ta PDP da amfani da karanci man fetur da ake fuskanta don ba ta mata suna a idon 'yan kasar.

  A wata sanarwa da kakakin Jami'iyyar Mallam Bolaji Abdullahi ya sanya wa hannu, APC ta ce tana sa ne da wahalhalun da 'yan Nigeria suka shiga sakamakon karancin man fetur musamman a lokacin bukukuwan kirsimeti.

  Sanarwar ta kara da cewa gwamnati tana iyakacin kokarinta don kawo karshen matsalar nan bada jima wa ba.

  Sai dai APC ta ce abun takaici ne yadda PDP take amfani da karancin man wajen bata sunan gwamnatin APC da jami'anta, abun da jam'iyyar ta ce ba siyace mai kyau ba.

  Tun da farko jam'iyyar adawa ta PDP ta kalubalanci shugaba Muhammadu Buhari da ya samar wa 'yan kasar man fetur ya daina zargin dillalan man da haddasa karancin da ake fuskanta.

  A wata sanarwa daga kakakinta Kola Ologbondiyan, PDP ta ce tun da shugaba Buhari ya nada kansa babban ministan mai, bai kamata ba ya rika zargin wasu da rashin wadata kasar da man fetur.

  PDP dai ta ce duk da alkawarin da APC ta yi cewa matsalar karancin man fetur za ta zama tarihi idan ta karbi mulki, halin kuncin da 'yan Nigeria suka shiga yanzu abu ne da ya nuna an yaudari 'yan kasar.  A Najeriya al’umma na ci gaba da kokawa kan matsanancin ƙarancin man fetur wanda ya shafi kusan ɗaukacin yankunan ƙasar.
  Hakan na zuwa ne a lokacin da al’umma da dama ke zirga-zirga sanadiyyar ƙaratowar bukuwan kirsimeti da na ƙarshen shekara.

  A Kano, jiha mafi yawan al’umma a ƙasar, mutane na sayen litar man fetur da tsada, inda a wasu wuraren ta zarta Naira 200.

  Muhammad Mujis, wani mazaunin birnin na Kano ya ce masu ababen hawa sukan yi doguwar tafiya zuwa ƙauyukan da ke wajen gari domin neman man fetur, yayin da ake samun dogayen layuka a ƙalilan daga cikin gidajen mai da ke sayar da man a cikin birni.

  Wata amarya da ta yanki mijinta da reza a goshi a ranar Juma’ar da ta gabata bayan daura aurensu da mako uku ta ce ba ta yi hakan da niyyar kashe shi ba.

  A ranar Juma’ar da ta gabata da dare ne amaryar mai suna Shafa Muhammad ta yanki angonta mai suna Umar Shehu wanda ya kai aka yi masa dinki sau biyu a Asibitin Koyarwa ta Usman dan Fodiyo da ke Sakkwato. 

  Ma’auratan suna zaune ne a Unguwar Arkillar Liman da ke karamar Hukumar Wammako a Jihar Sakkwato kafin faruwar lamarin.

  Amarya Shafa Muhammad mai shekara 20 a zantawarta da Aminiya a ofishin ’yan sanda na Arkilla inda ake tsare da ita ta bayyana auren da aka yi mata da cewa na tilas ne ba ta son mijin. Kuma tun kafin auren ta rubuta masa wasika cewa ita ba ta son sa kuma ta gaya masa ya bar zancen aurenta kada su aikata wani abu da zai sa mu yi da- na- sani amma bai ji ba Karanta saura >>>

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Labarai a yau Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });