• Labaran yau

  B-kebbi: Farashin man fetur N145 a A.A Rano, miye dalilin banbancin farashi a gidajen mai ?

  Isyaku Garba |

  An wayi gari da samun cinkoson babura a kofar shiga gidan mai na AA Rano a garin birnin Kebbi tare da dogon layi na motoci masu jira domin shan mai yayin da wasu gidajen mai babu masu sayen mai duk da yake akwai mai a cikinsu kuma suna sayer da mai ga mai bukata.

  Layin motoci ya fara daga gidan mai na A.A Rano da ke kan titin tsohon tasha ya kai har hanyar shiga unguwar Go Slow daga bangaren Asibitin Godiya  .

  Yayin da muka zagaya cikin garin Birnin kebbi, mun kula akwai mai a gidajen mai da dama musamman gangaren Illela Yari wadanda babu masu sayen mai amma an shaida mana cewa akwai mai.

  Bayanai sun nuna cewa cinkoso da dogon layin ababen hawa da aka gani suna jiran su sha mai a gidan mai na A.A. Rano ba zai rasa nassaba da rangwame da aka samu ba a yadda gidajen mai a garin Birnin kebbi ke sayar da mai.

  A.A Rano na sayar da mai akan N145 a kowane lita , yayin da yawancin gidajen mai ke sayarwa akan N190 ko N195 a kowane lita. Amma ko miye musabbabin wannan banbanci a farashin mai a garin Birnin kebbi ? yunkurin da muka yi domin mu samo amsa akan wannan ya ci tura domin wadanda ke da hakkin bayar da wannan amsa duka lambar wayoyin su na a kashe zuwa lokacin da muka rubuta wannan labari.

  Malam Aliyu Lawal wani mai mota ne wanda ke kan layi domin ya sha man fetur a gidan mai na A.A Rano ya shaida wa ISYAKU.COM cewa " Alhamdu Lillahi wannan bawan Allah da ke da wannan gidan mai yana tabbatar da cewa a ko da yaushe ana samar da mai a wannan gidan mai, mun shigo wannan layi da misalin karfe 8:00 na safe kuma nan kadan zan sami shiga domin in sha mai kamar yadda kake gani"

  "Mu kam a nan garin Birnin kebbi mun gode wa Allah da ya kawo mana shi a wannan jiha  watau A.A Rano idan ba don shi ba da abin da za'a shiga zai fi haka"

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: B-kebbi: Farashin man fetur N145 a A.A Rano, miye dalilin banbancin farashi a gidajen mai ? Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });