• Labaran yau

  Saurayi ya yanka wuyar budurwarsa, mata ta kashe maigida da guba a abinci

  Wani saurayi Abubakar Musa 'dan shekara 23 ya fada hannun 'yansanda a jihar Katsina bisa zargin yanka wuyar budurwarsa Aisha Dikkom da wuka.

  Kwamishinan 'yansanda na jihar Katsina Mr. Benson Gwana ya shaida wa manema labarai haka a Katsina ranar Asabar yayin da yake gabatar da wadanda ake zargin a gaban manema labarai.

  Ya kara da cewa wanda ake zargin ya dauki budurwarsa a kan babur daga karamar hukumar Charanci zuwa karamar hukumar Kurfi ranar 21 ga watan Disamba inda ya zagaya zuwa wani daji a kauyen Tamowa ya yanka wuyar budurwar tasa.

  Kwamishinan ya kara da cewa bayan saurayin ya aikata wannan 'danyan aikin sai ya tsere ya barta jini yana malala.

  Daga bisani wani bawan Allah ya tsinci yarinyar ya kai ta Asibiti aka dinke raunin wanda ya sa aka sanar da 'yansanda .Sakamakon haka aka kama Abubakar a unguwar  Sabon gari da ke garin Charanci.

  Kwamishinan ya shaida wa manema labarai cewa Abubakar ya amsa laifin sa ,ya ce ya aikata haka ne domin budurwar tashi tana shirin auren wani saurayi daban. 

  Haka zalika, hukumar ta 'yansanda a jihar ta Katsina ta kama wata mata Daushiya Abdullahi mai shekara 15 sakamakon zargin kashe mijin ta da abokinsa ta hanyar saka guba a cikin abincin su.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Saurayi ya yanka wuyar budurwarsa, mata ta kashe maigida da guba a abinci Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });