Labarai a yau Litinin 25/12/2017 (Safe)

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tausaya ‘Yan Najeriya kan halin kuncin da suka samu kan su sakamakon karancin man fetir da ya jefa al’ummar kasar cikin kuncin rayuwa.

A wasikar da ya rubutawa al’ummar kasar, shugaban ya ce yana bin halin da ake ciki sau da kafa, kuma yana samun bayanai daga kamfanin man NNPC kan kokarin da ake wajen shawo kan matsalar, inda ya ke cewa nan bada dadewa ba man zai wadata.

Jam’iyyar PDP mai adawa ta zargi shugaban da gazawa wajen karancin man musamman a wannan lokaci na bukukuwan kirsimeti da karhen shekara.

Shugaban kungiyar dattawan Igbo na Ohaneze John Nwodo ya ce da gan-gan gwamnati ta haifar da matsalar domin kuntatawa 'yan kabilar su.

Tsohon Ministan ilimi a Najeriya Oby Ezekwesili ta shawarci shugaba Buhari ya ajiye mukaminsa na Ministan Man kasar, inda ta ke cewa haka ne ka wai zai rage siyasar da fannin ke fuskanta.

Tun tsanantar wahalar Man 'yan Najeriya ke siyan litar guda na Fetir akan naira 400 zuwa 600 a wasu yankunan kasar.

Yayinda ‘yan Najeriya ke ci gaba da kokawa bisa karancin manfetur, wasu daga cikin ‘yan kasuwar da ke shigar da man daga kasashen ketare, sun bukaci gwamnatin kasar da ta tallafa, wajen saukaka musu samun dala bisa farashi mai rangwame, musamman domin basu damar ci gaba da shigo da man.
A cewar ‘yan kasuwar, a halin da ake ciki, ci gaba da saida litar manfetur guda bisa farashin naira 145, faduwa ce mai yawa a garesu, idan aka yi la’akari da farashin canjin naira da kudaden ketare.

Shugaban sashin ayyuka na kungiyar ‘yan kasuwar Najeriya masu shigar da man fetur kasar Mista Mike Osatuyi, ya ce, matsalar da ake fuskanta a yanzu ita ce, kamfanin man kasar NNPC ne kadai yake dauke da kusan kashi 100 na dawainiyar shigo da man, saboda janyewar da dama daga cikin ‘yan kasuwar, saboda yanayin farashin canjin kudaden.

Osatuyi ya ce a yanzu, idan suka yi amfani da kididdigar da ta kamata idan aka yi la'akari da karfin Naira kan kudaden kasashen waje, kamata yayi su rika sayar da litar man fetur a kan naira 154 muddin suna sayo shi a kan farashin naira 305 kan kowace dala guda.

Babban Shugaban Hukumar nan ta kididdiga wacce a Turance ake kira da, ‘Global Analytics,’ Mista Tope Fashua, ya shaidawa manema labarai cewa, yanda aka shirya da kuma yanda ake nufin kashe kasafin kudin shekarar 2018, ko kusa ba zai warware katuwar matsalar rashin aikin yi da ke addabar al’ummar wannan kasar ba, domin sam tsarin kasafin kudin bai dace ba, ba bu kuma wata fata ta gari a cikinsa.

A cewar sa, “Har ya zuwa yanzun, ana nan ana ta gabza mahawara a kan kasafin kudin a zaurukan Majalisun Tarayya, wanda daga bisani akwai kasantuwar yin gyaran fuska wa kasafin kudin, wanda hakan ke nufin, a karshe akwai yiwuwar samun sauyi a kasafin kudin.

“Amma a bisa la’akari da yadda ake amfani da hanyoyi irin na dauri, hakan yana nufin ba wani ci gaba da za a samu, face maimaita abin da aka saba maimaitawa kawai a baya. Hakan kuma yana tabbatar mana da kara samun marasa aikin yi ne kawai. Don haka, ba mu da sa ran gyara wannan matsalar da ke faruwa a yau, ta hanyar amfani da dubarun jiya. Karanta saura >>>

Sanata Kwankwaso yayi wadannan kalaman ne biyo bayan wata zungureriyar wasikar da sakataren jam’iyyar APC na kasa ya aike zuwa jihar wadda a ciki ya tabbatar da Injiniya Basie Yahaya Karats a matsayin shugaban jam’iyyar APC na riko a jihar Kano.

Injiniya Karats, wanda ake damfara shi da dan gaban goshin gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, wanda kuma ya karbi ragamar tafiyar da jam’iyyar APC daga Yerima Abdullahi Abbas; biyo bayan murabus da yayi yan kwanaki kadan da nada masa rigar kwamishina a jihar.

Kwankwaso ya kara da cewar “muna da masaniyar wata kuskuniyar sirrin karkashin kasa daga shugaban kasa Buhari ta hanyar mai taimaka masa a sha’anin hulda da kafafen yada labarai na gidajen rediyo, Ibrahim Shaaba Sharada, da wasu na kusa dashi, wajen cire shugaban APC da muka zaba a jihar, Haruna Umar Doguwa, ba tare da wata hujja daga kundin tsarin jam’iyyar APC ba. Karanta saura >>>

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN