• Labaran yau

  Karanta abin da Yombe ya fada a filin wasa na Haliru Abdu a B-kebbi

  Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai ya bayyana Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Abubakar Bagudu a matsayin haziki da ya zama gata ga matasa da al'umar jihar Kebbi sakamakon shirye-shiryensa na taimakawa matasa a fadin jiha tare da samun nassarori a kan harkar noma ,ilimi, kiwon lafiya tsaro da sauransu.

  Yombe ya yi wannan jawabi ne a filin wasa na Haliru Abdu da sanyin safiyar Lahadi yayin da yake a wajen da shahararrun tsoffin yan wasa Peter Rufai da Tijjani Babangida.wadanda Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya gaiyato domin su zakulo matasa 'yan wasa masu hikima daga cikin 'yan wasa na kulob-kulob na jihar Kebbi.

  Mataimakin Gwamna Samaila Yombe ya kara da cewa "Gwamnatin jihar Kebbi karkashin shuganmu Sanata Atiku Abubakar Bagudu ta bayar da kwangilar gina filayen wasanni a Masarautu hudu da ake da su a fadin jihar Kebbi kuma nan da 'yan watanni aikin zai kankama".

  Isyaku Garba Daga Birnin kebbi.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Karanta abin da Yombe ya fada a filin wasa na Haliru Abdu a B-kebbi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });