• Labaran yau

  Kwamishinan shari'a na jihar Kebbi bata yi murabus ba - Samaila Yombe

  Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai ya tabbatar cewa Kwamishinan Shari'a kuma babban Atoni janar na Ma'aikatar shari'a na jihar Kebbi Barr. Rukayyat Tanko Ayuba bata yi murabus ba kuma Gwamnantin jihar Kebbi bata dakatar da ita aiki ba sabanin labarai da suka bayyana a wasu shafukan labarai na yanar gizo dangane da lamarin.

  Alh. Samaila Yombe ya ce duk da yake za'a yi wani kwarya-kwaryar garambawul a mukaman Gwamnati amma ba wai yana nufin an dakatar da wani bane a mukamin sa kawo yanzu,garambawul ne da zai shafi ma'aikatu kamar yadda aka saba a al'adance game da tafiyar kowane Gwamnati a Najeriya.

  Ya kara da cewa har yanzu Barr. Rukayyat Tanko Ayuba ce Kwamishinan Shari'a na jihar Kebbi.Bisa wannan dalili ne ISYAKU.COM ke neman gafaran Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu da manyan jami'ansa da ita kanta Kwamishinan da labarin ya shafa Barr. Rukayyat da sauran masoya shafin mu akan wannan labarin da yawancin kafofin watsa labarai kamar Sun Newsonline, Daily Post ,Daily Trust da sauran jaridu suka wallafa.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kwamishinan shari'a na jihar Kebbi bata yi murabus ba - Samaila Yombe Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });