An karrama hazikan ma'aikata 23 na Filin jirgin saman Sir Ahmadu Bello B-Kebbi

Isyaku Garba |

An karrama wasu ma'aikata da suka nuna kwazo wajen gudanar da aiki a Filin sauka da tashin jiragen sama na Sir Ahmadu Bello wanda wakilin Gwamnan jihar Kebbi watau Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai ya gabatar da kyautuka ga zakarun ma'aikatan Filin Jirgin.

A bayanin gabatarwa da yayi Daraktan mulki na Filin jirgin ya ce wannan karramawa an yi shi saboda kwazo da ma'aikatan suka nuna domin ya zama kwarin gwuiwa ga sauran ma'aikatan.

Alh. Sha'aibu shugaban Airspace Management Agency NAMA ya ce akwai ma'aikata na jihar Kebbi sai kuma su NAMA wadanda jami'an Gwamnatin tarayya ne ya nuna irin aiki tukuru da ma'aikatan suke nunawa a wajen tafiyar da aikin su.

Ya kara da cewa godiya ce kawai zasu yi masu amma Allah da kanshi ne zai saka wa ma'aikatan da Alhairin sa.Ma'aikata 23 ne aka karrama, 9 daga hukumar NAMA yayin da 14 daga Gwamnatin jihar Kebbi.

Daga cikin wadanda aka karramma ta hanyar mika masu takardar yabo da ambulon da ke kunshe da ihsani sun hada da : Mal. Muhammed Abubakar, Murtala Muhammad, Mr Izeak Patrick, Mal Abubakar Umar Gege, Yahaya Abubakar Aliero, Raji Umar ,Aliyu Umar Dakingari ,Aliyu Liman tsohon soja mai mukamin saje, Mal Yahaya Abubakar Aliero HOD State.

Wadanda aka karrama daga bangaren jihar Kebbi sun hada da Bello Adamu, Nura Musa Gulma, Samaila B, da Abdulrasheed Sadauki da sauransu .

A jawabinsa na godiya Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh Samaila Yombe Dabai ya yi wa Allah Godiya na samun halartar taron tare da bayyana wakilcin sa ga Gwamna Sanata Atiku Bagudu .Ya kuma kara da cewa Allah da kanshi yana bukatar a gode masa,sakamakon haka karrama ma'aikatan da aka yi mataki ne da ya dace.

Yombe ya yi bayani akan muhimmancin aikin da ma'aikatan suke yi sakamakon haka kuma suke da matsayi na musamman ta la'akari da tsarin aikinsu.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.j

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN