'Dan shekara 49 ya kashe 'dan shekara 65 sakamakon duka da bulala

Rundunar 'yansanda a jihar Niger ta kama wani mutum 'dan shekara 49 mai suna Garba Tukura bisa zargin kashe makwabcinsa mai suna Musa Wasa 'dan shekara 65 a kauyen Zazzagawa na karamar hukumar Munya.

Kakakin hukumar 'yansanda na jihar Niger Peter Sunday ya ce yayin wata zafaffar musanyar kalamai ne Tukura ya yi amfani da bel na injin ya dinga zabga wa Wasa lamari da ya sa Wasa ya fadi ya suma kuma daga bisani aka garzaya da shi Asibiti inda ya mutu.

Kakakin yansandan ya ce bayan an shaida wa 'yansanda lamarin ne ya sa 'yansanda da ke ofishin su na Sarkin Fawa suka kama Tukura. Peter Sunday ya shaida wa Northern City News cewa za a gurfanar da Tukura a gaban Kotu.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN