• Labaran yau

  Labaran Duniya Juma'a 15/12/2017

  An hana wata 'yar Najeriya da ta kammala karatun lauya zama lauya - mai iya aiki a kotu - saboda hijabin da ta saka wanda ake ganin ya saba wa dokar tufafin makarantar horars da lauyoyin kasar.

  Shugaban makarantar horas da lauyoyi Isa Hayatu Chiroma ya shaida wa BBC cewa an hana Amasa Firdaus shiga dakin taron yaye lauyoyi ne saboda bata sanya tufafin da ya dace ba.

  Ta ki ta cire hijabinta, tana mai cewa dole ta saka hular lauyoyi kan dan-kwalinta, in ji shafin intanet na Nigerianlawyer.com.

  Rahotanni sun ce Firdaus ta bayyana matakin a matsayin wani abin da ya keta hakkinta na bil Adama.

  Wata kotun soji a Najeriya ta yanke hukuncin kisa a kan wani jami'in sojin kasar bayan kama shi da laifin kisan wasu fararen hula a yankin arewa maso gabashi da ake yaki da Boko Haram.

  Kotun sojin ta musamman a Maiduguri ta zartar da hukuncin ne kan koforal John Godwin da ta samu da laifin kisan fararen hula biyar da sojoji suka kubutar a garin Yamteke.

  Jami'in wanda yana cikin rundunar Lafiya Dole da ke fada da Boko Haram, ya harbe mutanen ne a garin Maiduguri, a yayin da ake tsare da su domin amsa tambayoyi.

  A cikin sanarwar da rundunar sojin Najeriya ta fitar ta ce kotun ta kuma daure wani jami'in soja rai da rai mai suna Innocent Ototo wanda kotun ta samu da laifin azabtarwa da kisan wani yaro dan shekaru 13 bayan jami'in ya zarge shi da sace wayarsa ta salula a Maiduguri.

  Sannan kotun ta kuma zartar da hukuncin daurin shekaru 20 a kan wasu jami'an soja guda biyu kan laifin kisa da mallakar makamai ta hanyar da ba ta dace ba.

  Rundunar sojin Najeriya ta ce laifukan da jami'an suka aikata sun saba dokokin kasa da na duniya.
  Kungiyoyin kare hakkin bil'adama na gida da na waje dai sun dade suna zargin sojojin Najeriya da kashewa da kuma cin zarafin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, zargin da rundunar sojin kasar ta sha musantawa.

  Majiya daga ma’aikatar kudin Najeriya ta bayyana cewa an bai wa wadanda suka taimaka wa hukumar yaki da rashawa ta EFCC da bayanai domin gano makuddan kudade a wani gida da ke unguwar Ikoyi a Lagos kudin ladarsu da suka Naira milyan 421.

  Tun bayan da Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar EFCC, da ta gaggauta bayyana mamallakan makuden kudaden da yawansu ya kai Dala Miliyan 43, wanda aka gano a wani kasaitaccen gida da ke unguwar Ikoyi a jihar Legas.

  Sai dai hukumar ta EFCC ta sake samame a gidan, in da a wannan karo ta binciki sassan tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi da kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP mai adawa, Alhaji Ahmad Adamu Mu’azu.

  Wannan na zuwa ne bayan wasu jami’an leken asiri sun ce, akwai yiwuwar an boye wasu kudaden daban a sassan gidan.

  Rahotanni da dumi-duminsu na cewa an samu salwantar rayuka a wani wurin da ake hakar ma'adinai sanadiyar arangama da masu hakar ma'adinan suka yi da 'yan sandan jihar ta Taraba.

  Ta bakin kakakin 'yan sandan jihar David Misal, masu hakar ma'adinan da yanzu aka ayyana su a matsayin masu aiwatar da haramtaccen aiki sun kwashe shekara da shekaru suna aikin a yankin. Sai kwana kwanan nan da gwamnatin jihar ta ce su daina sai sun nemi izini daga gwamnatin.

  Kokarin da 'yan sanda suka yi na ganin mutanen sun bar wurin sun kuma daina aikin hakar ma'adinan ya jawo hargitsi tsakaninsu da mutanen. Inji kakakin 'yan sandan DSP David Misal da ya zanta da Muryar Amurka, maimakon mutanen su saurari bayani sai suka fara jifa tare da duka, lamarin da ya jawo hargitsi tsakaninsu ke nan.

  Dangane da adadin rayukan da suka salwanta, kakakin ya ce suna ci gaba da tattara bayanai amma mutane biyu sun mutu, daya daga kowane bangare.

  A cewarsa wadanda suka jikata an kaisu gidan shan magani inda ake yi masu jinya.
  Al'ummar yankin suna zargin cewa gwamnati ta baiwa wani kamfanin waje wurin nasu domin ya ci gaba da hakar ma'adinan maimakon a yi da su saboda kasar tasu ce kana su kansu sun dade suna aikin.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Labaran Duniya Juma'a 15/12/2017 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });