• Labaran yau

  Motar 'yan amarya ta yi hatsari, mata 11 sun mutu, 2 suna asibiti

  Mata 11 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani mumunar hatsarin mota da ya rutsa da su ranar Asabar yayin da suka dauko wata Amarya kan hanyarsu ta zuwa gidan mijinta a birnin Kano.

  Mai magana da yawun rundunar kiyaye hadurra na kasa (FRSC) reshen jihar Kano Mr. Kabir Ibrahim Daura ya ce lamarin ya faru da misalin karfe 8:30 na daren ranar ta Asabar yayin da wata mota ta dauko 'yan rakiyan Amarya daga Unguwa Uku zuwa 'Yan Lemu.

  Mr. Kabir ya kara da cewa direban yana cikin matsanancin gudu ne sai motar ta kwace masa daga bisani ya yi karo da tsohuwar ginin tsoron toll gate kusa da Kwalejin koyar da ilimi na Sa'adatu Abubakar Rimi, kuma nan take mata 8 suka mutu bayan motar ta rabu gida biyu sakamakon hatsarin, daga bisani wasu matan guda 3 suka mutu a Asibiti.

  Direban motar da wani yaron mota basu mutu ba a cikin hatsarin kuma suna karbar magani a Asibiti.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Motar 'yan amarya ta yi hatsari, mata 11 sun mutu, 2 suna asibiti Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });