Yadda aka yi tarzoma a gadar kasuwar Wuse sakamakon kashe wani direba

An yi tarzoma a gadar kasuwar Wuse da ke babban birnin tarayya Abuja ranar Laraba lamari da ya sa jami'an tsaro na Abuja Task Force suka tsere daga gurin.

Wasu rahotanni da suka fito daga birnin Abuja sun nuna cewa lamarin ya faru ne yayin da wani mutun ya je wajen matarsa wadda take sana'a a kasuwar ta Wuse kuma ya tsayar da motarsa a gefen titi ya zauna yana cin abinci.

Daga bisani jami'an Task Force suka zo akan lamarin motar da aka ajiye a gefen titi, amma sai zafafan gardama ya kaure tsakanin jami'an da direban motar.Sakamakon haka ana zargin cewa wani jami'i a cikin jami'an tsaron ya bindige direban kuma ya mutu nan take.

Ganin haka ke da wuya jama'a suka yi tarzoma suka kona tayoyi yayin da jami'an tsaro da ke a Task Force suka ranta na kare. Masu tarzoman sun gungura wata motar daukan motoci na VIO zuwa gangaren titi na kasuwar ta Wuse suka jefar da motar. 

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN