• Labaran yau

  'Yan fashi 10 sun tsere daga hannun 'yan sanda

  Akalla wadanda ake tuhuma da aikata laifi mutum goma ne suka tsere daga kurkukun 'yansanda sashen SARS a hedikwatar 'yansanda da ke Yenegoa na jihar Bayelsa.

  Amma wasu rahotanni sun nuna cewa an sake kama biyar daga cikin mutum goma da suka tsere.An kama mutanen ne a Yenegoa  yayin da aka kama sauran a Agbura wanda ke daga gefen birnin Yenagoa ranar Talata.

  Bayanai sun nuna cewa hakan ya faru ne bayan Kwamishinan 'yansanda na jihar ta Bayelsa ya bayar da umarni cewa ala tilas a nemo wadanda suka tseren.

  Wata majiya ta labarta cewa wani dakiki da ke cikin wadanda aka tsaren mai suna Touch-Touch shi ne ya yanke karfen windo na kurkukun chaji ofis wanda daga bisani ya bi ta silin kuma ya fice ba tare da masu aikin dare sun gan shi ba.

  Wasu masu gadi a karamar hukumar Yenagoa ne suka kai rahotu bayan sun kula wasu mutane sun ketare katangar hedikwatar yansanda wanda ke makwabta da ofishin karamar hukumar ta Yenagoa da misalin karfe 10:00pm.

  Mai magana da yawun hukumar 'yansanda na jihar Bayelsa Mr. Asinim Butswat ya tabbatar da faruwar lamarin .

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: 'Yan fashi 10 sun tsere daga hannun 'yan sanda Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });