• Labaran yau

  Musulmi sun tone gawar da tsawa ya kashe ta bayan kwana 47

  Musulmi a garin Oro na jihar Kwara sun tone gawar wani Ma'aikacin Gwamnatin jihar Kwara Salami Adekunle wanda tsawa ta kashe shi yayin da ake ruwan sama kwanaki 47 da suka gabata. Bayan rasuwar Salami wasu mabiya addinin gargajiya na Yarbawa sun gudanar da wasu tsafe-tsafe a gawar Salami kuma suka shafa masa jinin Alade da Kare lamarin da ya sa aka ki yarda a bizine gawar a Makabartar Musulmi a garin Oro.

  Bisa wannan dalilin aka bizine Salami a wata Makabarta wadda ba ta Musulmi ba. Wannan lamarin ya sa wasu Musulmi bayin Allah suka kalubalanci yadda aka yi wa gawar Salami inda suka bukaci a basu dama domin su tone gawarsa.

  Daga bisani hukumomi a jihar ta Kwara sun basu dama suka tone gawar bayan kwana 47 kuma aka sami gawar tsaf kuma suka wanke ta suka yi mata sutura ta Musulunci daga bisani aka bizine ta bisa tsarin Musulunci kuma a Makabartar Musulmi a jana'iza da ya sami halartar dubban al'umma Musulmi sakamakon sanarwa da aka yi a Masallatai. Limamin Masallacin jami'ar Illorin Prof. A.G.À.S Oladosu ne ya jagoranci Sallar jana'izan.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Musulmi sun tone gawar da tsawa ya kashe ta bayan kwana 47 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama