NSCDC ta kama wadanda suka yi wa 'yar shekara 5 fyade suka yi luwadi da yayanta a Argungu

Daga Isyaku Garba |

Yanzu haka hukumar NSCDC ta jihar Kebbi tana gudanar da bincike akan zargi da ake wa wasu mutum biyu bisa laifin aikata fyade ga wata 'yar karamar yarinya 'yar shakara 5 da aikata luwadi ga wani yaro mai shakara 13 wanda yaya ne ga karamar yarinyar da ake zargin an yi wa fyade.

Bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru ne a unguwar Makarantar Sama Royal Primary School a garin Argungu. Wani abin mamaki shine yadda wasu suka dinga alakanta uwar wadannan yara da ciwon hauka ko sida bayan ta bayyana zargin abin da ya faru ga diyanta.

Wadannan yara da Mahaifiyarsu wanda a zahiri talakawa ne suna cikin matsanancin damuwa sakamakon abin da ya faru da su.Shi dai wannan yaro kurma ne, yarinyar kuma karama ce 'yar shekara 5.

Mahaifiyarsu mai suna sa'a Abubakar ta shaida wa manema labarai cewa bayan da aka yi wa yarinyar fyade, wadanda suka aikata wannan danyen aiki sun shafa wa yaran Acid a lebon bakin su da idanun sawun kafafun su lamari da ya haifar da gazawar fitar da kalamai domin yin magana ko sarrafa jiki yadda ya kamata.

Malama Sa'a ta kara da cewa hatta a cikin maclean na goge baki an saka mata wannan Acid wanda bayan ta yi amfani da shi wajen goge baki daga bisani fuskan ta ya kumbura kuma ta shiga wani hali domin tana ta jin yanayi da cewa kan ta yana ta juyawa.

Bincike ya nuna cewa Mahukunta a rundunar NSCDC ta jihar Kebbi sun sha alwashin tabbatar da gaskiya a cikin wannan lamarin da ya sami kulawan babban Kwamandan rundunar ta jihar Kebbi shi da kanshi wanda ya bayar da umarni kai tsaye da a gaggauta kammala bincike domin a gabatar da wadanda ake tuhumar a gaban Kotu.

Wata majiya ta shaida mana cewa wannan matar Sa'a Abubakar ta fuskanci jifa'ai kala kala ciki har da kayakinta da aka kona da ruwan batur da kazafi cewa mahaukaciya ce ko tana da kanjamau da sauransu.Amma a zantawar mu da ita babu wata alama nan take da ke iya tabbatar da kasancewarta mahaukaciya.

Yanzu haka Sakataren kungiyar Mata 'yan jarida na Arewa maso yammacin Najeriya Khadijah Sa'idu tare da hadin guiwa da kungiyar Lauyoyi Mata na Najeriya sun shiga gaba domin ganin wannan yarinya 'yar shekara 5 da yayanta 'dan shekara 13 sun sami adalci kan keta darajar rayuwarsu da aka yi.Haka zalika kungiyar 'yan jarida ta jihar Kebbi tana biye da lamarin da idon basira.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN