Karin bayani kan masoya da suka mutu bayan sun yi zina a cikin mota (Hotuna)

An sami karin bayani dangane da labarin da muka ruwaito na wani mutum da wata mata da suka mutu a cikin mota bayan sun gama yin zina a unguwar Ogba na jihar Lagos.Wani rahotu da muka samu ya bayyana sunan mutumin Olowo Lukman Olayinka yayin da sunan matar Nse Promise Nnena ranar Lahadi.

Haka zalika rahotun ya nuna cewa dukan mamatan suna zaune ne a cikin gida daya wadda kowa ke da sashensa, kuma tabbas matar dana da aure har da yara hudu kuma maigidan matar abokin Olowo ne wanda tayi zina da shi kuma makwabcin maigidanta.

Lamarin ya daure wa mazauna gidan kai bayan labarin abinda ya faru ya zo kunnuwansu ganin cewa dukan mamatan suna zaune lafiya a cikin wannan babban gida wadda kowane magidanci ke zaune a nashi bangare kuma mahaifin Olowo ne ke da mallakin gidan.

Kakakin hukumar yansanda na jihar Lagos Olarinde Famous-Cole ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da yace hukumar tana jiran sakamakon gwajin musabbabin mutuwar Olowu da Promise daga Likitan  binciken Gawa.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN