Domin na yi wa diyata fyade ba lalurar ku ba ce - uba da ya yi wa diyarsa fyade

Wata babban Kotun tarayya a garin Lagos ta adana wani mutum mai suna  Agu Echezona Harrison dan shekara 37 a gidan yari bisa zargin yi wa diyarsa 'yar shekara 6 fyade ta hanyar saka yatsunsa a al'auran yarinyar.

'Dansanda mai gabatar da kara Adebayo Haroun ya shaida wa Kotun cewa lamarin ya faru ne tsakanin 2013 zuwa 2015 a gida mai lamba 23 Rotimi Omotosho Street, Isheri Osun na jihar Lagos.

Matar Agu  mai suna Akukwe Priscilla wadda shaida ce a shari'ar ta shaida wa Kotu cewa ta lura cewa wani farin ruwa mai warin gaske yana fitowa daga al'auran yarinyar kuma sakamakon bincike da ta yi ya nuna cewa diyar ta shaida mata cewa mahaifinta Agu shi ne yake saka yatsarsa a cikin al'aurar ta.

Haka zalika ta yi zargin cewa a 'yan shekarun baya hatta kanwar ta ma Agu ya yi mata fyade, amma aka boye zancen saboda matsala ce ta cikin gida.

Yayin da Manema Labarai suka yi kokarin ji ta bakinsa dangane da lamarin Agu ya yi barazanar cewa zai gurfanar da su a gaban Kotu idan suka rubuta wani labari dangane da lamarin."Wannan matsalata ce ta cikin gida saboda haka ba lalurar ku bace". Hatta wani 'dan jarida na NAN da ya yi kokarin ya dauki hotonsa ,Agu ya watsa masa piya-wata kuma ya tashi ya rufe fuskarsa kamar yadda ya bayyana a hoton wannan labari.

Kotu ta dage shari'ar har zuwa ranar 20 ga watan Nowamba yayin da ake ci gaba da tsare Agu a gidan yari.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN