• Labaran yau

  Gwamnatin Najeriya za ta biya N88b ga wadanda yakin Biafra ya rutasa da su (Hotuna)

  Isyaku Garba |

  Gwamnatin Najeriya ta aminta za ta biya zunzurutun kudi har Naira Biliyan 88 ga wadanda yakin Biafra ya rutsa da su shekara 47da suka gabata. Za'a yi amfani da kudaden wajen lalata sauran nakiyoyi da bama-bamai da ke watse a cikin dajin wannan yanki da yakin ya shafa.

  Za'a yi amfani da Naira Biliyan 38 domin biyan 'yan kwangila da za su tafiyar da aikin share burbushin da sauran nakiyoyi da bamabamai a yankin yayin da za'a yi amfani da Naira Biliyan 50 wajen biyan hakikanin wadanda yakin ya rutsa da su daga 1967 zuwa 1970.

  Kotun kasashen yammacin Africa ECOWAS ta aminta da shirin wanda ya samo asali bayan Vincent Agu ya gurfanar da Gwamnatin tarayyar Najeriya a gaban Kotun a 2012 amma Gwamnati ta bukaci a sasanta lamarin a wajen Kotu.

  Jihohi da za su amfana da kudaden sun hada da Anambra, Rivers, Akwa Ibom, Delta, Ebonyi, Cross River, Abia, Enugu da jihar Benue.


  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Gwamnatin Najeriya za ta biya N88b ga wadanda yakin Biafra ya rutasa da su (Hotuna) Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama