• Labaran yau

  NDE ta ce za ta ci gaba da lalata bututum man fetur a Najeriya

  Kungiyar tsageru masu tayar da kayar baya na yankin Niger Delta watau Niger Delta Avengers NDA ta ce zata maido da tashin hankali,kone-kone,kashe kashe da lalata bututun mai a fadin yankin har sai Gwamnatin Najeriya ta basu 'yancin cin gashin kansu.

  Sanarwar haka ya fito daga hannun wakilin kungiyar  Mudoch Agbinibo wanda aka fi sani da suna "GENERAL".

  A bara ne dai kungiyar ta tsagaita wuta domin ta baiwa Pan Niger Delta Forum, PANDEF dama ta yi sulhu da Gwamnatin Najeriya,General ya ce amma PANDEF ta gaza ci ma muradun al'umman yankin bisa kuduri da suka gabatar wa Gwamnati wadda bai haifar da sakamako da suke bukata  ba.

  Ya ce bisa wannan hujja ne suka kaddamar da wannan sabon hari kuma sun yi waje da Chief Edwin Clark da tsohon shugaban 'yan tawaye Government Ekpemupolo wanda ake wa aka fi sani  da suna Tompolo a cikin tsarinsu.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: NDE ta ce za ta ci gaba da lalata bututum man fetur a Najeriya Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama