• Labaran yau

  'Dan shekara 43 ya roki Alkali ya kai shi gidan Yari

  Wani mutum mai suna Saburi Yusuf 'dan shekara 43 ya roki Alkalin wani Kotun Majestare cewa don Allah ya tura shi gidan yari .Yusuf yana fuskantar tuhumar bata motar wani mutum da gangan a gaban Kotun.

  Bayan da mai gabatar da kara Inspector Olakunle Shonibare ya gabatar da karan gaban Kotu , Alkalin Majestare Idowu Olayinka ya tambayi Yusuf ko haka lamarin yake ? inda Yusuf ya amsa cewa haka ne.Alkali ya tambaye Yusuf ko zai iya biyan wanda ya yi wa barna domin kada ya je gidan yari amma sai Yusuf ya ce shi fa ya gwammace ya je gidan yari domin baya da wata hanyar da zai sami kudin da zai biya mai motar.

  Ana zargin Yusuf da lalata jikin wata mota Opel Sintra za'a kashe kimanin N38.000 kafin a gyara,da farfasa gilashin motar kimanin N25.000 da gilasan kofofin motar kimanin N30.000 wanda mallakin wani  Tunde Olalaye ne. Lamarin ya faru a kauyen Adu kan hanyar OGTV/Ajebo a garin Abeokuta.

  An tasa keyar Yusuf zuwa gidan yari har sai ranar 26 ga watan Janairu 2018 kafin a ci gaba da shari'ar.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: 'Dan shekara 43 ya roki Alkali ya kai shi gidan Yari Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama