• Labaran yau

  Sanata Dino Melaye ya sha ruwan duwatsu a Kabba na jihar Kogi

  Sanata mai wakiltar Kogi ta yamma Dino Melaye ya ketare rijiya da baya sakamakon ruwan duwatsu da wasu Matasa suka yi masa wajen bikin ranar Kabba a jihar Kogi.

  Melaye ya isa wajen taron da misalin karfe 11:00 na safe ranar Asabar inda ya sami gagarumin maraba daga magoya bayansa.

  Daga bisani aka bukaci Sanatan ya yi jawabi inda yayi amfani da wannan damar ya bayar da gudunmuwar N3m.Wannan ya faru ne kafin isowar Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello wanda shi ma yana cikin garin Kabba domin halartar taron.

  Bayan da Sanatan ya gama jawabinsa kuma ya nufi wajen motarsa domin ya bar wajen taron sai wasu matasa suka fara jifarsa da duwatsu, piya wata ,da sauran abin da hannunsu ya iya dauka.

  Nan take Sanatan ya samu kariya daga 'yansanda da ke tare da shi da sauran jami'an tsaro da magoya bayansa.Daga bisani 'yansanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa suka tarwatsa matasan kuma aka maido da zaman lafiya yayin da aka kama wani 'dan daba guda daya.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Sanata Dino Melaye ya sha ruwan duwatsu a Kabba na jihar Kogi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama