• Labaran yau

  Hukumar 'yansanda ta kori wani kofur bisa zargin yi wa 'yar shekara 14 fyade

  Hukumar 'yansanda ta Najeriya ta kori wani Corporal Barau Garba 'dan shekara 46 daga bakin aiki bisa samunsa da laifin yi wa wata yarinya 'yar shekara 14 fyade a jihar Anambra.

  Wannan ya biyo bayan wani hukunci na cikin gida na Orderly Room da Barau ya fuskanta inda aka same shi da laifin aikata laifin da ya saba wa aikin 'dansanda kuma nan take aka kore shi daga bakin aikinsa na 'dansanda daga ranar30 ga watan Oktoba.

  Rahotanni sun nuna cewa ana zargin Barau da tsare yarinyar a cikin dakinsa har kwana shida inda ya yi ta yi mata fyade bisa ra'ayinsa.

  Kakakin hukumar 'yansanda na jihar Anambra Mrs. Nkiruka Nwode ta tabbatar da koran Corporal Barau Garba daga aikin 'dansanda ta kara da cewa rundunar za ta gurfanar da Barau a gaban Kotun Majestare a ranar 8 ga watan Nowamba bisa tuhumar yin fyade.

  Kafin aukuwar lamarin Barau yana aiki ne da sahen 'yansandan kwantar da tarzoma Mopol 7 Sokoto kuma an tura shi jihar Anambara ne bisa ayyuka na musamman kuma aka kai shi caji ofis na Okpoko a garin Onitsha.


  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Hukumar 'yansanda ta kori wani kofur bisa zargin yi wa 'yar shekara 14 fyade Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama