Rainin ya fara yawa: Gwamna Fayose kirista a cikin sahun Sallar Juma'a (Hotuna)

Duk da cece-kuce da caa da al'umma Musulmi suka yi masa sa'ilin da ya yi shiga irin ta Musulmi ya kuma sallaci idi tare da Musulmi,Gwamna Ayo Fayose na jihar Ekiti har'ila yau ya sake takalo magana yayin da aka ganshi kane-kane a sahun gaba rike da carbi alhalin ana cikin gabatar da Sallar Juma'a jiya a babban Masallacin Juma'a na jihar Ekiti.

Ranar Juma'a da ta gabata ne Fayose yake cika shekara uku akan karagar mulki da ke cike da jan magana harma da abinda wasu ke ganin cewa nuna rashin ragowa ne ga dattijo irin shugaba Buhari sakamakon rashin sanya wa kalamansa burki  yayin da yake caccakar jam'yar APC mai mulki ko manufofinta.

Bayan da aka kammala Sallar Juma'a Fayose ya yi amfani da wannan dama ya gabatar da bayanai masu karfin gaske wadda ke da nassaba da siyasa .

Wani jigo a wata kungiya ta addinin Musulunci Muslim Rights Concern MURIC Farfesa Ishaq Akintola ya takankado wa Fayose kalamai da suka yi daidai da abinda ya aikata yayinda Farfesa Ishak yace al'umma Musulmi ba zasu ci gaba da jure wa irin wannan wulakanci da raini da Fayose ke yi ba akan Addinin Musulunci.

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Hoto:nationalhelm 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN