'Dan giya ya mance motarsa a gidan giya ya yi kara wa 'yansanda cewa an sace motar

A ranar Juma'a da ta gabata wani mutum mai suna Jude wanda 'dan giya ne na gaske ya kwankwadi barasa kuma yayi tatil a kauyen Anthony daga bisani ya share da barci.Bayan ya farka sai ya garzaya caji ofis ya kai rahotu akan cewa an sace motarsa kirar Toyota Camry 2010 model.

Bayan jami'an 'yan sanda sun kula cewa Jude yayi tatil da giya ne sai suka adana shi inda ya kara sharewa da barci daga bisani suka je gurin da yace ya kwankwadi barasa sai suka gan motar da Jude yace masu an sace pake a wajen ajiye mota 'yan mitoci kadan daga mashayar.

'Yan sanda sun tsare Jude na takaitaccen lokaci daga bisani aka sami kwararru suka bashi shawarwari kafin aka bar Jude ya tafi gida.

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN