Har yanzu tasirin barnar beraye ya hana Buhari yin aiki a babban ofishinsa

Har yanzu annobar beraye sun hana shugaba Buhari gudanar da aikinsa daga cikin babban ofishinsa a fadar shugaban kasa kusan wata biyu bayan dawowarsa daga hutun jinya a kasar Britaniya inda ya share kusan kwana dari domin fuskantar kulawa daga Likitocinsa bisa lalurar jinya.

Bayan dawowarsa gida Najeriya sakamakon murmurewa da yayi,shugaba Buhari yaci karo da cikas sakamakon barna da akace beraye da sauran kwari suka yi wa babban ofishinsa a fadar ta shugaban kasa lamarin da yasa yake gudanar da ayyukansa daga wani ofis cikin ofis ofis da ake da su a fadar ta shugaban kasa.

Wani hadimin shugaba Buhari watau  Garba Shehu yace har yanzu ba'a kammala aikace aikacen gyara ga babban ofishin shugaban ba amma an matsa wa kamfanin da ke gudanar da aikin akan ya sa himma domin ganin an kammala aikin a bisa ka'idar lokaci.

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN