Matsafan bogi sun shiga hannun 'yansanda

Wasu matasa sun shiga hannun rundunar 'yansanda na jihar Osun bayan an zarge su da kasancewa Matsafan karya wata dabara da suke amfani domin su yi cuta wa jamaa'a ta hanyar karban kudade daga gurin su.Wadanda aka kama sun hada da Yusuf Taofeek dan shekara 21 da Jimoh Sherif 20.

Wasu 'yan banga da suke sintiri ne suka kama wadanda ake zargin a magamar Jomodo a unguwar Ifon-Osun kafin su mika su ga 'yansanda.

Kwamishinan 'yansanda na jihar Osun yace wadanda aka kama sun shahara wajen damfaran mutane ta hanyar yin camfe-camfe da sambatu domin su damfari jama'a cewa zasu yi masu kudi.Ya kara da cewa rundunarsa za ta gabatar da su a gaban Kotu.

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN