Koko: Kungiyar Izala ta yi kira a inganta tarbiyya da kadaita Allah

An yi kira ga al'ummar musulmi da suyi riko da Tauhidi da sunnar ma'aiki Sallallahu alaihi wasallam. barin shirka, rikon amana da tsare hakki tsakanin kowace Al'umma. Sheikh Abdurrahman Isah jega shugaban Majalisar Malamai na Jahar Kebbi ya jaddada haka a lokacin da yake gabatar da nasa wa'azi wurin wa'azin da kungiyar Jama'atul izalatil bid'ah wa'ikamatis-sunnah mai hedikwata a Jos ta gudanar a daren jiya Assabar 07/10/2017 a cikin garin Koko na jihar kebbi. 

Daruruwan al'ummar jihar Kebbi da makwabatan jihar suka sami halartar taron wa'azin. Daga cikin abinda Malaman suka gabatar sun hada da Tauhidi kadaita Allah shi daya, tarbiyya, kyawawan 'dabi'u da halaye, inda anan ne suka fi mayar da hankali.

Manyan Malaman da suka halarci wa'azin sun hada da Sheikh Abdurrahman Isah jega, Sheikh Yusuf Sarkin malaman Yauri, Sheikh Usman Abubakar Damana, Sheikh Abdullahi Khaleel Dagwala Koko , Alhafiz Muhammad Abubakar Ribah saura kuma sun hada da Malam Ibrahim Malabil ,Malam Rabi'u Tafawa Balewa, Malam Kabiru Bala koko da sauran su.

Daga Aminu Musa Liman Koko


Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN