• Labaran yau

  B-kebbi: Mi ya banbanta wasan Nura M.Inuwa da na wasu mawaka a Kebbi ?

  Fitaccen mawakin Hausa Nura M.Inuwa ya gudanar da wasa a filin wasa na Sakatariyar Haliru Abdu da ke garin Birnin kebbi da yammacin yau Lahadi a yanayi na cashewa, kadekade daga fayafai da raye-raye wadda ya sami halartar 'yan mata da samari da suka  zo domin su gan Mawakin.

  Duk da yake an fara wasan da yamma sosai a yanayi da duhu ya fara bayya,bugu da kari samari da 'yan mata sun bar kujerunsu domin su matsa kusa da Mawakin saboda su sami sukunin daukan bidiyo da hotunansa.

  Yusuf Ali wani saurayi ne daga unguwar Badariya a cikin garin Birnin kebbi wadda yake a filin wasan ya shaida mana cewa "Ni dai ban ji dadin yadda aka tsara wannan wasan ba sakamakon rashin abin da Mawakin zai hau domin kowa ya ganshi cikin sauki.Bai kamata ace na kasance a tsaye ba bayan na biya N500 domin na gan wasa amma ka gan sakamakon rashin tsari yadda aka bar mutane a tsaye har ma matsa mana ake yi cewa mu ja baya wanda haka bai kamata ba".

  Yayin da ISYAKU.COM ya yi kokarin dauko hotunan mawakin wasu jami'ai sun hana a tsaya a dakalin da mawakin yake bisa hujjar cewa suna da nasu 'yan jarida.Sakamakon haka ya sa muka hada namu ya namu muka fice daga wajen wasan.

  Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: B-kebbi: Mi ya banbanta wasan Nura M.Inuwa da na wasu mawaka a Kebbi ? Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });