Fasinjoji a wata motar haya sun kashe wani safeton 'yansanda bayan ya harbe wani fasinja har lahira tare da raunata wani fasinja sakamakon zafafar musanyar kalamai bayan safeton ya ki karban N50 da direba ya ba shi.
Lamarin ya faru ne a Wuro-Dole a karamar hukumar Girei na jihar Adamawa ranar Laraba.
Bayanai sun nuna cewa safeton tare da wani 'dansanda sun sanya shinge inda suke tare ababen hawa domin bincike,ana zargin cewa safeton ya bukaci na goro daga direban motar wadda ya bashi N50 shi kuma safeto ya ce ala tilas sai an bashi N100.
Bisa wannan hujja wani fasinja ya kalubalanci safeto amma kaddara ta riga fata domin safeto ya harzuka matuka lamarinda yasa ya harbe mutumin nan take tare da raunata daya daga cikin fasinja.
Gani haka ke da wuya sai safeton ya yar da bindigar ya ruga da gudu.
Fasinjoji suka bi shi da gudu suka kama shi kuma suka yi masa ruwan duwatsu ta hanyar jifa har ya mutu.
Kakakin hukumar 'yansanda na jihar Adamawa Othman Abubakar ya tabbatar da faruwan lamarin ga manema labarai.
Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Tags:
LABARI