'Yan kungiyar IPOB sun kashe 'dan sanda sun yi awon gaba da bindigogi

Labarai da ke fitowa daga jihar Rivers sun nuna cewa kungiyar nan ta kabilar Igbo makiya zama lafiya IPOB ta kai farmaki a sashen rundunar 'yansandan ko ta kwana (Mopol) a magamar Oyigbo inda suka kashe 'dansanda daya Sgt. Steven Daniel  tare da jikata mutum biyu.Maharan sun kuma yi awon gaba da bindigar 'dansandan.

Wannan ya faru ne bayan a jiya 'yan kungiyar ta IPOB sun kai wa wata motar 'yansanda farmaki akan hanyar filin jirgin sama na Port Harcourt inda suka kona motar kurmus tare da jikata wadanda ke cikinta daga bisani suka yi awon gaba da bindiga kirar AK 47 da albarushi 60,da karamar bindigar hannu Pistol da albarusai guda takwas.

Kwamishinan 'yansanda na jihar Rivers Zaki M.Ahmad ya shaida wa manema labarai cewa rundunar ta kama batagari 'yan kungiyar ta IPOB 32 kuma suna taimaka wa rundunar wajen bincike.Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN