Malaman tsibbu sun dukufa a kai na - Isyaku Garba

Kowane dan adam tara ne bai cika goma ba,haka zalika tunani,fahimta ko basira ba daya bane tsakanin mutane.A ci gaba da takaddama wadda ya samo asali da kin gaskiya,kyashi,hassada da rashin wadataccen ilimin lissafin ka'ida a rayuwa.A yau mun bayyana a Kotu.

Saboda haka ina rokon jama'ar da suka yi ta bayar da hakuri cewa ku ma don Allah ku yi hakuri saboda ko Manzon Allah SAW ya ce ba'a saran Mumini sau biyu a rami daya.Ni an sare ni fiye da yadda ya kamata kuma hakurin ne ya janyo raini.

Ni dai ban shigo Birnin kebbi tallar Gwanjo ba,dan asalin jihar Kebbi ne ni,amma abin tausayi shine yadda zunduki yayi nassarar tarwatsa hadin kan 'yan jihar Kebbi.Inda za ka gane bakar aniyar wannan annoban rahama shine duk da wadata da ya samu a Birnin kebbi har yanzu bai auri 'yar Birnin kebbi ba amma wani ya gaya mini cewa dole ne a sami matsaloli domin tun farko TAMKAR tamu ba daya bace.

Ina kira ga duk yara na da masoya na akan cewa kada su wulakanta ko su raina wani domin mu ba al'adar mu bane,ba gadon mu bane kuma ba zamu koya ba a rana tsaka.

Jama'a ku ji irin wannan labarin,dazu da yamma wani bawan Allah ya tsegunta mini yadda wani da ya kirkiro damuwa tsakanin mu ya kai sunana a wajen Malamin tsibbu,har an sayo barkono da allurai da turare kuma suna can suna yin Yasin !...haba Malam ashe wanna Mushiriki ne ! gaske dai yake kin gaskiya zahiri.

Ni na dogara ga ALLAH .Kuma ina rokon duk masoyina ya taya ni rokon Allah ya kare ni daga Mushirikai da Matsafa.


Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN