Labarin wani Sarki mai hikima

A zamanin da ,a Birnin Fahshar an yi wani Sarki mai suna Sultamari wanda mulkinsa cike yake da adalci da son daidaita gaskiya a tsakanin al'umma.

Wata rana sai manyan mutane a garin kamar su Waziri, Ubandawaki, Shamaki, Shantali da dai sauransu suka je gurin Sarki Sultamari a yayinda yake a cikin gonar Lambunsa inda yake hutawa sai suka fadi suka yi gaisuwa.

Sarki ya amsa gaisuwarsu sai yace da Waziri yau lafiya kuwa aka biyo ni har cikin Lambu? Waziri yace Lafiya kalau ran Sarki ya dade face sun zo ne da wata bukata guda daya amadadin jama'ar gari.

Sarki yace to miye wannan bukatar? Waziri ya shaida masa cewa sun kula cewa Karuwai sun yi yawa a garin kuma hakan zai iya bata masu yara da tarbiyyar su.

Sai Sarki yace ku dakata ina zuwa, sai ya tashi ya dauki buta ya je ya kama ruwa sai ya dawo ya zauna ya cire hula ya yi alwala sai ya dauko Alkur'ani ya daga yayi rantsuwa da Allah cewa shi bai taba yin ZINA ba kuma yana son kowane mutum a cikinsu ya tashi ya yi Alwala ya yi rantsuwa akan cewa bai taba yin zina ba tunda Mahaifiyarshi ta haife shi.

Gabadaya dai babu wanda ya iya yin abin da Sarki ya yi....sai Sarki yace ku tashi ku tafi ku tarbiyantar da kanku da 'ya'yanku.


Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN