Fulani ya mutu sakamakon duka a wajen Sharo

A kauyen Durmin Biri a karamar hukumar Kafur na jihar Katsina wani saurayi Fulani  mai suna Yari Inusa ya rasa ransa wajen sharo bayan abokin takararsa a wajen sharon Ahmed Saidu ya shade shi a kai cikin kuskure lamarinda ya sa Yari ya yanke jiki  ya fadi nan take.

Bayan faduwarsa daga bisani an tabbatar da cewa Yari dai ya rasu sakamakon raunin duka a kansa,kuma hakan ya sa Mahaifinsa ya kai kara a wajen 'yansanda wadda hakan ya kai ga kama Ahmed.

Kakakin hukumar 'yansanda na jihar Katsina DSP Gambo Isah ya tabbatar da aukuwar lamarin ,ya kuma kara da cewa an bayar da gawar Yari ga Iyayensa domin a yi  masa jana'iza yayinda ake ci gaba da bincike akan lamarin.

Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Hoto: Travelhobnigeria 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN