Rahotanni daga kasar China sun nuna cewa hukumomi a yammacin yankin Xinjiang suna ci gaba da tsanantawa tare da gallazawa al'umma Musulmi a wani kamfen da hukumomin suka ce mataki ne na kalubalantar harkokin 'yan ta'adda.
Gidan radiyo na Radio Free Asia ta labarta cewa lamarin ya fi kamari a yankunan Kashgar, da Hotan inda mahukuntan suka dinga kwace sallaya da Alkur'anai har da charbi daga hannayen Musulmi lamarin da ya janyo hukunci mai tsanani ga duk Musulmin da bai bayar da wadannan ababen ba.
Wata majiya ta labarta cewa hukumomi a Xinjiang suna karbe kofi na Kur'anai da aka wallafa su tun shekara biyar da suka gabata a lamari da ta kira " kokarin dakile ayyukan 'yan ta'adda".
Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Tags:
LABARI