An kama Pasto da yayi batanci ga Musulunci

Gwamnatin kasar Seirra Leone ta kama wani Pasto dan Najeriya mazauni kasar ta Seirra Leone Victor Ajisafe bayan ya yi kalaman batanci ga addinin Musulunci a jawabin wa'azi da yayi wa masu bauta a Chocin sa The Sanctuary Praise Church ranar lahadi.

Ajisafe ya ce "Musulunci addinin tashin hankaline, karya da cuta.Musulmai ne ke aikata ta'addanci a tarihin Duniya" wadannan kalamai nan take suka zagaya a shafukan sada zumunta lamarin da ya janyo hankalin Gwamnati kuma daga bisani aka kamashi.

Duk da yake bayanai sun nuna cewa ba'a tuhume shi ba kawo yanzu amma yana tsare a hannun hukumomi a kasar.

Sakamakon wani bincike da cibiyar Pew ta gudanar a 2015 ya nuna cewa Musulmi su ne kashi 78% na al'umman kasar ta Seirra Leone.

Shugaban sashen manyan laifuka na kasar (CID) MB Kamara yace "Seirra Leone kasa ce da babu banbancin addini kuma sudai basu san irin wannan banbancin ba , saboda haka kalaman wannan Pasto dan Najeriya ba kalamai da zasu lamunta da su ne ba a Seirra Leone"


Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN