B-kebbi: Fulani ya sare kan abokinsa akan hanyar Kalgo

Rundunar 'yansanda a jihar Kebbi ta kama wani Fulani mai suna Umar Muhammad dan shekara 23 wadda ake zargi da sare kan abokinsa sakamakon rigima akan wani Sa wadda shi Umar ya sayar ba bisa izini ba.

Kakakin hukumar 'yansanda na jihar Kebbi DSP Suleiman Mustapha ya shaida wa manema labarai haka ranar Talata a garin Birnin kebbi.

Ya kara da cewa Umar ya kashe Mustapha Muhammed dan shekara 22 yayin da yake barci a wani gini da ba'a kammala ba a hanyar Kalgo.

Rigimar ta samo asali ne bayan Umar ya sayar da wani shanu da aka basu kiwo ba tare da izini ba kuma wannan shine karo na biyu,sakamakon haka Mustapha ya kalubalanci Umar daga bisani kuma yayi barazanar cewa zai shaida wa mai shanun yadda Umar yayi da shanunsa.

Sakamakon haka Umar ya fakaici Mustapha yayin da yake barci sai ya sare masa kai.Majiyar tamu ta ci gaba da cewa Umar ya koma gida ba tare da Mustapha ba kuma da aka tambaye shi sai  yace ai ya baro shi a daji.

Bayan an fara nemansa a daji an gano gawar Mustapha har ta fara rubewa babu kai.Da aka tsananta bincike Umar ya nuna inda ya binne kan Mustaha kwanaki uku bayan aukuwar lamarin.

"Zamu gabatar da wadda ake zargi gaban Kotu da zarar an kammala bincike" inji kakakin hukumar 'yansanda DSP Mustapha Suleiman.

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN