Yaro ya banka wa abokinsa wuta sakamakon bacewar wayar salula

Wani karamin yaro mai suna Junior Onah yana kwance a Asibiti rai hannun Allah bayan wani yaro Wisdom Kelechi ya banka masa wuta sakamakon bacewar wayar salularsa a wajen Junior.

Lamarin ya faru a garin Enugu ranar Litinin.Bayanai sun nuna cewa Kelechi ya je wani shagon aski inda ya sami Junior kuma ya saka wayar salularsa domin ta yi chaji a shagon da yake tsammani Junior zai taimake shi domin ya fake masa wayarsa a unguwar Ifoh file a cikin Abakpa Nike na jihar ta Enugu.

Daga bisani Kelechi ya dawo sai bai gan wayar ba saboda haka ya tambayi Junior ko ina wayarsa take domin bai ganta a wajenda take chaji ba shi kuma Junior yace shi kam bai dauki wayar ba.Nan take Kelechi ya fita ya dawo da galon na fetur inda ya zuba wa Junior kuma ya kunna masa wuta da ashana.

Kakakin hukumar 'yansanda na jihar Enugu Ebere Amaraizu ya tabbatar da faruwar lamarin ,ya kuma kara haske akan cewa an garzaya Asibiti da Junior inda yake jinya sakamakon munanan kuna da ya samu yayin da rundunar ta kama Kelechi nan take kuma yana taimaka masu a bincike da suke yi.

Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN