'Yan bindiga sun kashe mutane da dama lokacin ibada a Choci

Da sanyin safiyar yau Lahadi wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su waye ba suka kai hari a Chocin St. Philips Catholic Church a Ozubulu na jihar  Anambra.

Hukumar 'yansanda a jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin inda Kwamishinan 'yansanda na jihar Mr Garba Umar ya tabbatar cewa 'yan bindigan sun shiga Chocin ne kuma suka yi ta harbin mai uwa da wabi.

Kwamishinan ya kara da cewa mutane da dama sun mutu da yawa kuma sun sami raunuka inda ake yi masu magani a Asibitin koyarwa na Nnamdi Azikiwe da ke garin Nnewi.Ya kuma ce musabbabin tashin hankalin ba zai rasa nassaba da ayyuka na gungun masu aikkata laifi da ke gaba da juna ba.


Ku biyo mu a
https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN