• Labaran yau

  Shugaba Buhari ya yi wa jama'ar Anambra jaje kan harin Choci

  Shugaba Muhammadu  Buhari ya tattauna da Gwamna  Willie Obiano na jihar Anambra ta wayan tarho inda ya jajanta masa tare da jama'ar jihar Anambra akan kisan gilla  da wasu da ba'a san ko  su waye ba suka kai a wani Choci inda harin ya halaka mutane da dama wasu kuma suka jikata.

  A wani bayani da ya fito daga hannun mai taimaka wa shugaban kasa kan harkar jarida da hulda da jama'a Garba Shehu yace"Shugaba Buhari ya tausayawa wadanda lamarin ya rutsa da su kuma wannan ya nuna irin rashin imani da salo wadda wasu suka dauka domin suyi fada da zaman lafiyan 'yan Najeriya wadda Gwamnatinsa ba zata lamunta ba".

  Shugaba Buhari ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa Gwamnatinsa zata yi iya kokarinta domin ta tabbatar da mutunci da lafiyarsu.
  Ku biyo mu a
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Shugaba Buhari ya yi wa jama'ar Anambra jaje kan harin Choci Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama