B-Kebbi: "muhimmancin shayar da jariri nonon uwa har wata 6"- UNICEF

Asusun kula da yara kanana na majalisar dinkin duniya reshen jihar Kebbi tare da hadin gwuiwar sashen Lafiya da ilmantar da al'umma na karamar hukumar Birninkebbi sun gudanar da tattaki don shelar wayar da kan al'umma domin ganin an shayar da jarirai nonon uwa har tsawon wata uku.

Tattakin wanda ya bi da su ta wasu muhimman titunan garin Birnin kebbi,wasu daga cikin masu tattakin dauke da kwalaye da ke dauke da rubuce-rubuce da ke kira ga uwaye su dinga shayar da jariransu nono har tsawon wata shida.

Mr.Nathaniel Rocks daya ne daga cikin wadanda suke jagorancin tattakin ya shaida mana cewa kamar yadda muke gani tattakin hadin gwuiwa ne da Gwamnatin jihar Kebbi da karamar hukumar Birnin kebbi,kungiyoyi da sauran masu aikin sa kai don gabadaya su kara wayar da kan jama'a musamman uwaye mata akan muhimmancin shayar da jariri nonon uwa har tsawon wata shida.

Nathaniel ya kara da cewa tun lokacin da kwamiti suka fara aiki a jihar Kebbi ya gano cewa wasu uwaye basa shayar da jarirai nonon uwa har tsawon wata uku,domin akasari sukan hada da ba jariri ruwa marmakin nono zalla wanda a cewarsa hakan yakan iya haifar da illa ga lafiyar jariri nan gaba.
 


Ku biyo mu a
https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN