Ma'aikatan Majalisar dokoki na jihar Kebbi sun fara yajin aiki

A ranar Litinin Ma'aikatan Majalisar dokoki na jihar Kebbi sun fara yajin aiki saboda rashin biyansu hakkokin su na alawus har tsawon shekara uku.

Rahotanni sun nuna cewa Ma'aikatan sunyi ta ihu suna furta kalamai da ke nuna cewa a biya su hakkinsu lamarin da yasa alatilas 'yan Majalisar suka kasa ci gaba da zamansu na Majalisa.

A wani bayani da yayi wa manema labarai  Alhaji Mohammed Garba wadda shine Ciyaman na  kungiyar ma'aikatan Majalisun dokoki na Najeriya yace sunyi iya abinda ya kamata domin su lallabi hukumomin da abin ya shafa su biya su hakkin su a cinkin shekaru 3 da suka gabata amma basu ci ma nassara ba.

Alh.Garba yace suna kyautata zaton cewa za'a shawo kan lamarin a cikin lokaci kalilan tunda Gwamnatin jihar Kebbi tayi alkawarin cewa zata duba lamarin da idon basira.




Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN